Ko Kasan ‘Yanwasan Da Za Su Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe?

Yayin da ya rage saura kwanaki kaɗan a fara gasar cin kofin duniya da aka sauyawa fasali zuwa ƙasashe 48 wadda kuma za a kece raini a ƙasashen Amurka da Canada da kuma Meɗico.
Kawo yanzu an samnu dukkan ƙasashen da za su buga wasannin, har da waɗanda a karon farko za su buga babbar gasar ta duniya a tarihi. Wannan gasar za a yi tata-ɓurza ganin tawagogin suna da yawa, an ƙara yawan wasanni da filaye da jami’an da za su gudanar da gasar ta 2026.
Argentina ce mai riƙe da kofin da ta ɗauka a shekarar 2022 a Ƙatar, kenan Messi zai yi fatan kare kofin daga nan ya rataye takalmansa. Wasannin bana za a samu matasan da za su nuna kansu da kuma waɗanda tsuka yi tsufan da wannan ce gasar da za su halarta ta ƙarshe.
A nan ga jerin wasu ƴan wasan da za su buga gasar ƙarshe a cin kofin duniya a 2026.
Nahiyar Turai: Cristaino Ronaldo da Luca Modric da Keɓin De Bruyne da Dani Carɓajal da Ɓirgil ɓan Dijk da Granit Ɗhaka da kuma Eden Dzeko.
Nahiyar Kudancin Amurka: Lionel Messi da Neymar da James Rodriguez da Luis Suarez
Africa: Mohamed Salah da Sadio Mane da Kalidou Koulibaly da Riyad Mahrez da kuma Ɓozinha.
Nahiyar Asia: Son Heung-Min da kuma Wataru Endo.
Nahiyar Oceania: Chris Wood
Cristiano Ronaldo (Portugal)
Cristiano Ronaldo shi ne mutum na farko da ya ci ƙwallo a gasar FIFA World Cup guda biyar daban-daban ya nuna irin daɗewar da ya yi da irin wannan bajintar da ya yi. Duk da ƙalubalen da ya fuskanta a gasar 2022 da ta kai an yi waje da su a zagayen kwata fainal, har yana nuna ƙwazo duk da yawan shekarunsa.
Idan ya kai ga buga gasar 2026, Ronaldo zai shiga gasar yana da shekara 41, wanda hakan zai zama tarihi na bayyana a kofin duniya karo na shida. Lashe babbar kofin duniya ne ya rage masa a kundin nasarorinsa, kenan damar da yake da ita a bana kenan, daga nan zai haƙura da ziyartar gasar cin kofin duniya.
Luka Modric (Croatia)
Bayan da ya ja ragamar ƙasarsa mai mutane miliyan huɗu zuwa wasan ƙarshe da kuma matsayi na uku a gasar FIFA World Cup biyu a jere a shekarar 2018 da 2022, wani babban abin tarihi ne da ya saka, wanda yake da gogewa.
Luka Modric ya zama ginshiƙin nasarorin Croatia tun bayan da ya fara buga mata tamaula a duniya shekara 20 da suka gabata a gasar da aka gudanar a Jamus.
Zai shiga gasar 2026 yana da shekaru 40, wataƙila gasa ta ƙarshe a rayuwarsa, wanda ya lashe kyautar Golden Ball a gasar kofin duniya ta 2018 a Rasha.
Keɓin De Bruyne (Belgium)
Sai kuma ɗan wasa Keɓin De Bruyne, rashin kai wa wasan ƙarshe a gasar 2018 FIFA World Cup tare da Belgium har yanzu yana daga cikin abubuwan da ke damun ɗan wasan da ya yi fice a gasar Premier League a lokacin ƙololuwar wasansa. Cika shekaru 35 yayin gasar kofin duniya ta 2026 na nufin ɗan wasan zai iya kasancewa ya jagoranci ƙasar karo na ƙarshe a babbar gasar ta duniya.
Dani Carɓajal (Sifaniya)
Duk da cewa ɗan wasan mai shekara 34 na fama da rauni ana shakku ko zai iya buga wasannin bana kuwa? Dani Carɓajal gogagge ne a jagorancin Sifaniya yayin da take neman ƙarin wata babbar nasara a matakin duniya.
Lashe kofin Champions League da dama tare da Real Madrid bai kai ga ya samu nasara a gasar FIFA World Cup ba a rayuwarsa ta ƙasa da ƙasa. Saboda yawan shekarunsa da kuma yawan fama da rauni — wataƙila wannan ce gasar kofin duniya ta ƙarshe da mai tsaron bayan Real Madrid ɗin zai halarta.
Ɓirgil ɓan Dijk (Netherlands)
Kyaftin ɗin tawagar Netherlands ya ja ragamar ƙasar zuwa matakin kusa da na kusa da na ƙarshe a gasar 2022 FIFA World Cup. Ɓirgil ɓan Dijk mai shekaru 34 yana matuƙar son ganin ƙasarsa ta yi wani abu a gasar da za a buga a Arewacin Amurka, kuma zai jagoranci matasan tawagar Netherlands zuwa lashe kofin bana da ɗan wasan Liɓerpool ke fatan halartar gasar kofin duniya ta ƙarshe.
Granit Ɗhaka (Switzerland)
Ƙoƙarin da Switzerland ke nunawa a manyan gasa ta duniya ya haɗa daga jagoranci da kuma ƙwarewar Ɗhaka da kyaftin ɗin tawagar da ya daɗe yana yi wa ƙasar. Ɗhaka ya halarci gasar FIFA World Cup sau uku a baya, hakan wata alama ce da ke nuna cewa gasar ƙarshe da zai halarta kenan, wanda ke fama da jinya a yanzu haka.
Wannan gasar ta 2026 yana da shekara 33, yayin da yake fama da jinya, watkila jikin ne ya gaji, ya kamata ya rataye takalmansa da zarar an kammala gasar kofin duniya ta bana.
Edin Dzeko (Bosnia and Herzegoɓina)
Tsohon ɗan wasa Dzeko shi ma ya zo ƙarshe, bayan rawar da ya taka da ta kai sun yi waje da Italy a wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya a watan Maris, magoya bayan Bosnia and Herzegoɓina na kallon fitaccen mai cin ƙwallon a matsayin jagoran dawo da ƙasar zuwa babban matakin duniya fiye da shekara goma bayan bayyanarsu ta farko a 2014.
Yawan cin ƙwallayen da ya yi a manyan lig-lig a Turai bai rage kishin wannan gwarzon mai shekaru 40 ba, wanda aka saka shi cikin jerin ƴan wasa 26 da za su halarci gasar 2026 FIFA World Cup a ranar 11 ga watan Mayu. Jagorantar ƙasarsa a matsayin kyaftin a 2026 zai zama cikakken bankwana a tarihi Edin Dzeko, ɗan wasan da ya zama alamar ƙwallon ƙafar Bosnia.
Lionel Messi Argentina
Lashe gasar 2022 FIFA World Cup a ƙasar Ƙatar da Messi yayi, ta tabbatar da matsayin shi a matsayin ɗaya daga cikin mafi girman ƴan wasan ƙwallon ƙafa da duniya ta taɓa gani a wannan lokacin.
Ɗaukar kofin duniya da Messi ya yi abin kamar al’amara bayan da tawagar ta fara da rashin nasara, daga baya ta kai ga lashe kofin, wanda ya fara zuwa gasar kofin duniya a 2006 tun yana matashi.
Duk da cewa ana tsammanin zai yi ritaya bayan gasar 2022, sai kawai ya ci gaba da kasancewarsa cikin tawagar Argentina yana da shekaru 38, amma ana hasashen cewar gasar 2026 za ta iya zama ta ƙarshe da zai wakilci ƙasarsa a tarihi. Jan ragamar Argentina zuwa gasar da za a buga a Arewacin Amurka zai bai wa tauraron Inter Miami ɗin damar yin bankwana da ƙwallon ƙafa a ƙasar da yanzu take matsayin gidansa na wasanni wato Amurka.
Neymar (Brazil)
Ƙasar Brazil ta cika da murna da shewa bayan da kociyan tawagar Carlo Ancelotti ya bayya na sunan Neymar a cikin jerin ƴanwasan da za su wakilci ƙasar a gasar cin kofin duniya kuma hakan ya nuna cewa zai sake bayyana a babban matakin gasar ta duniya karo na ƙarshe.
Yawaitar raunuka sau da yawa ya hana ɗan wasan gaba na Santos FC nuna cikakken tasirinsa a lokutan da tawagar ta Brazil ta fi buƙatar hakan a matakan ƙarshe na gasar.
A baya Neymar ya taɓa bayyana cewa gasar 2022 za ta iya zama ta ƙarshe a gare shi, amma burin lashe kofin duniya na shida da Brazil ke fata, mai shekaru 34 ya sake yin yunƙuri na ƙarshe, domin a kafa wannan tarihin tare da shi. Kenan zai so ya gyara kurakuren da ya tafka da samun lashe kofin duniya, domin a ci gaba da tunawa da shi a fannin ƙwallon ƙafa a duniya.
James Rodriguez (Colombia)
Yayin da ƴan wasa da dama suke nuna kansu a gasar kofin duniya, James Rodriguez mai shekara 34 ya kafa tarihin da har yanzu ana hangen abin da ya yi a 2014.
A lokacin yana da shekaru 24, ɗan wasan na Colombia ya jagoranci ƙasarsa zuwa matakin kwata-fainal, inda ya ci ƙwallaye shida da lashe kyautar Golden Boot.
Ɗaya daga cikin ƙwallayen da ya ci na ban mamaki har da wata wadda ya ci Uruguay a zagayen ƴan 16, wanda har yanzu ake ɗauka a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun ƙwallaye da aka zura a raga na ban mamaki a tarihin kofin duniya. Wannan gasa za ta kasance ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka kasance a rayuwar James da kuma tarihin ƙwallon ƙafar Colombia baki ɗaya.
Luis Suarez (Uruguay)
Bayan da ya jawo cece-kuce a watan Satumba da iƙirarin cewa Marcelo Bielsa ya raba kan ƴan wasan ƙasar, daga nan makomar Luis Suarez tare da tawagar Uruguay ta fara zama cikin shakku. Duk da cewa yiwuwar sake buga wata gasar FIFA World Cup na iya zama mai wahala, ɗan wasan mai shekara 39 ya sake komawa kan ganiya da hakan kan iya ba shi damar buga gasar karo na biyar bayan 2010 da 2014 da 2018 da kuma 2022.
Wasanninsa biyu a gasar sun yi ƙaurin suna saboda hannu da ya sa a lokacin da Ghana za ta ci su a ƙarin lokaci a kwata-fainal na 2010, yayin da a 2014 kuma ya shiga cikin rikicin bayan da ya ciji ɗan ƙasar Italy, Giorgio Chiellini. Duk da cewa ba wanda ya goyi bayan abin da ya yi, har yanzu ana jiran ganin ko Bielsa zai sake gayyatar tsohon ɗan wasan tawagar, domin yiwuwar bankwana ta ƙarshe a gasar duniya.
Mohamed Salah (Egypt)
Ƙwallon ƙafar ƙasar Masar ta samu ci gaba mai yawa saboda wani fitaccen ɗan wasan gaba da ke ɗauke da burin kai ƙasar a kan ƙololuwa a Afirka da duniya gabaki ɗaya.
Mohamed Salah ya halarci gasar FIFA World Cup ta 2018 duk da yana fama da rauni, abin da ya hana duniya ganin cikakken bajintarsa a wasannin. Amma komawarsa gasar 2026 — wacce za ta kasance karo na huɗu a tarihi — za ta yi fatan taka rawar gani a karon farko fiye da wasannin da ta halarta a baya. Shigarsa cikin shekara 30 na nufin wannan ka iya zama dama ta ƙarshe ga Salah, domin ya bar tarihi a gasar kofin duniya.
A yanzu dai baya kan ganiya kamar da, kasancewar Sadio Mané a gasar FIFA World Cup ta 2026 a Arewacin Amurka ana ganin ita ce ta karshe da zai halarta.
Yanzu yana da shekaru 34, ɗan wasan tawagar Senegal yana cikin tawagar “Lions of Teranga” da ta fice daga gasar 2018 a matakin rukuni bisa ƙididdigar fair play points, sannan a 2022 suka kai zagaye ƴan 16 kafin Ingila ta doke su da ci 3-0.
Wannan tarihin yana nuna irin ci gaban da Senegal ta samu a gasar kofin duniya, tare da yiwuwar gasar 2026 ta zama bankwana ga ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasanta na zamani.
Kalidou Koulibaly (Senegal)
Kalidou Koulibaly ya tabbatar da matsayinsa na gwarzo a ƙasar Senegal bayan da ya jagoranci “Teranga Lions” a matsayin ƙyaftin wajen lashe kofin Africa Cup of Nations da kuma kai wa matakin fitar da gwani a gasar FIFA World Cup ta 2022.
Fuskantar manyan ƴan gaba na duniya a gasar 2026 ya ba shi damar ƙarshe — yana da shekaru 34 — don nuna irin ƙwarewa da ƙarfinsa a matakin ƙwallon ƙafa a duniya.
Wannan na iya zama babi na ƙarshe ga ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan tsaron bayan Senegal a zamaninsa.
Riyad Mahrez (Algeria)
Riyad Mahrez zai halarci gasar kofin duniya karo na biyu — kuma mai yiwuwa ta ƙarshe — a gasar FIFA World Cup, bayan shekara 12 da ya fara shiga gasar a 2014.
A wancan lokacin, tsohon kocin Algeria Ɓahid Halilhodžić an ruwaito cewa ya fuskanci zargin rashin gaskiya ta yadda ya shigar da Mahrez cikin tawagar a 2014, kodayake irin waɗannan batutuwa babu su a cikin tawagar da Ɓladimir Petkoɓić zai jagoranta a gasar da za a buga a Arewacin Amurka.
Yanzu yana da shekaru 35, Mahrez na iya shiga gasar ne a matsayin ɗaya daga cikin gogaggun ƴan wasa a abin da zai iya zama bankwana da babbar gasar ƙwallon ƙafa ta duniya.
Ɓozinha (Cape Ɓerde)
Ɓozinha, mai tsaron raga na Cape Ɓerde, zai yi murnar cika shekaru 40 a lokacin gasar FIFA World Cup, abin da ke nuna irin tsufansa a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƴan wasa mafi shekaru a tarihin gasar.
Kasancewarsa muhimmi kuma ginshiƙi ga wata ƙasa da za ta shiga gasar a karon farko a tarihi ya ƙara bayyana muhimmancinsa ga tawagar Cape Ɓerde. Wannan hali na gogaggen mai tsaron raga na nuna yadda ƙwarewa duk da yawan shekarunsa, wanda ke kan ganiya a taka rawa a matakin duniya, musamman ga ƙananan ƙasashe masu tasowa a ƙwallon kafa.
Guillermo Ochoa (Meɗico)
Magoya bayan Meɗico sun saba ganin fitaccen mai tsaron ragarsu, yana zama tamkar katanga a kowace gasar FIFA World Cup da ake yi duk bayan shekara huɗu. Wannan gogaggen mai tsaron gida ya yi suna ta hanyar tare ƙwallaye su shiga raga masu ban mamaki da manyan ƴan gaba ke nuna fasaharsu a duniya, ya buga gasar 2014 da 2018 da kuma ta 2022, tare da kasancewa cikin tawagar a 2006 da 2010 ba tare da buga wasa ko ɗaya ba.
ƙoƙarin samun shiga tawagar gasar kofin duniya karo na shida zai sanya Guillermo Ochoa cikin rukunin ƴan wasa na musamman a tarihin gasar. Kenan a wannan gasar da Meɗico ma ke karɓar baƙunci, zai samu yin ban kwana da tawagar Meɗico, wacce ake kira “El Tri”.
Johnny Placide (Haiti)
Johnny Placide na daga cikin ƴan wasa mafi gogewa da ake sa ran za su halarci gasar kofin duniya, inda mai tsaron ragar ƙasar ta Haiti ya taka muhimmiyar rawa a dukkanin matakan neman tikitin shiga gasar bana. Ɗan wasan mai shekaru 38 ya nuna ƙwarewa da jagoranci, wanda ya taimaka wajen tabbatar da tsaron baya da kuma ɗorewar ƙwazon tawagar Haiti a lokacin wasannin share fagen shiga gasar.
Ƙwarewarsa da hangen nesa a filin wasa sun sa ya zama ginshiƙi ga tawagar, musamman a lokutan da aka fi buƙatar kwanciyar hankali da gogewa a manyan wasanni.
Son Heung-Min (South Korea)
Son Heung-min ya nuna tasiri mai girma a tawagar Koriya ta Kudu bayan da ya taka rawar gani wajen doke Portugal a gasar FIFA World Cup ta 2022. Yin wasa duk da raunin da ya ji a fuska a lokacin gasar ya nuna irin jajircewarsa da sadaukarwa, abin da ya sa ya zama gwarzon ƙasar.
Idan ya kai ga shiga gasar 2026 yana da shekaru 33, hakan na iya zama dama ta ƙarshe ga ɗan wasan Los Angeles FC ta Amurka, domin jagorantar Koriya ta Kudu zuwa matakan ƙarshe a gasar cin kofin duniya.
Wataru Endo (Japan)
Wataru Endo ya kasance ɗaya daga cikin muhimman ƴan wasa a tawagar Japan da ta yi nasara mai tarihi a kan Jamus da Sifaniya a gasar FIFA World Cup ta 2022.
A wannan gasar a Ƙatar, Japan ta nuna kishin ƙasa da jajircewa ta yadda ta sanarwa duniya, kowa ya iya buga wasa a duniya ba kamar a baya ba, kafin a taka an san gwani.
Shigarsa gasar 2026 yana da shekaru 33 na nuna cewa wannan ka iya zama babi na ƙarshe a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa ta ƙasa da ƙasa, wacce ta ginu bisa aiki tuƙuru da ladabi.
Chris Wood (New Zealand)
New Zealand za ta koma buga gasar FIFA World Cup bayan shafe shekara 16 ba ta halarta ba, inda hakan ya ba wani fitaccen ɗan gaba mai shekaru 34 damar samun damar da ya daɗe yana jira.
Chris Wood, wanda shi ne mai riƙe da tarihin yawan cin ƙwallaye a tarihin ƙasar, zai jagoranci tawagar a babbar gasar ƙwallon ƙafa ta duniya da za a buga a Amurka da Canada da kuma Meɗico.
Ƙwarewar da yake da ita a gasar Premier League ta Ingila ta zama muhimmiyar ginshiƙi ga tawaga da za ta sake buga gasar kofin duniya a karo na farko tun bayan 2010. Idan ya samu damar zura ƙwallo a wannan mataki, hakan zai zama cikar mafarki ga ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan da New Zealand ta taɓa samarwa.



